✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sayar da kalmomin farko da aka wallafa a shafin Twitter kan dala miliyan 2.9

A makon jiya ne mai kamfanin sada zumunta na Twitter, Jack Dorsey, ya sayar da rubutun farko da aka fara wallafawa a shafin kan kudi…

A makon jiya ne mai kamfanin sada zumunta na Twitter, Jack Dorsey, ya sayar da rubutun farko da aka fara wallafawa a shafin kan kudi Dala miliyan 2.9, kimanin Naira biliyan daya da rabi.

Mista Jack ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani sako da ya wallafa a shafinsa yana mai cewa a sayar da rubutun ne mai dauke da kalmomi kacal ga wani attajiri dan kasar Malaysia mai suna Sina Estavi.

Rubutun da aka sayar mai dauke da kalaman “just setting up my twttr”, sun kasance kalmomin farko da Mista Jack ya wallafa bayan kaddamar da Manhajar Twitter a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2006.

An yi wannan ciniki ne ta hanyar kudin intanet wato sulallan Crypto bayan makonni biyu da sanya gwanjon kalmomin kamar yadda wani rahoto na jaridar USA Today ya nuna.

Bayan wannan ciniki, wani abun mamaki da ya kara jan hankalin al’umma shi ne yadda Mista Dorsey ya sadaukar da kudin ga Nahiyyar Afirka domin tallafa mata wajen rage radadin annobar Coronavirus.

A wani sako da Mista Dorsey ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce kai tsaye kudin zai tafi asusun Kamfanin jin kai na Give Directly mai tallafa wa talakawa da marasa galihu da ke ci gaba da fuskantar radadin Coronavirus a kasashen Kenya, Liberia, Rwanda, Malawi, Jamhuriyyar Congo da Togo.