✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shawarci Buhari ya mayar da farashin man fetur zuwa N302 duk lita

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ne ya gabatar da rahoton a kan shawarar.

Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya mayar da farashin man fetur zuwa naira 302 duk lita.

A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin naira 162 da 165 a kan kowace lita.

Sai dai duba da wannan shawara da Majalisar Tattalin Arzikin ta bayar tun a watan Nuwambar bara, akwai yiwuwar gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai kamawa na Fabrairu.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa tana ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannunta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.

Kwamitin wucin-gadi naMmajalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.

Bayanai sun ce Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton yayin da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da ke zaman Shugaban Majalisar Tattalin Arzikin ya jagoranci zaman da aka yi a Nuwamba na bara.