✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soke dokar hukunta ’yan daudu da masu sauya jinsi a Kuwait

Maha al-Mutairi, mai shekara 40, wani dan daudu da ya mayar da kansa mace da ke cin sarka.

Kotun Tsarin Mulki ta Kuwait ta soke dokar da ta haramta daudanci ko mace ta rika kwaikwayon namiji, wadda kuma ake amfani da ita wajen hukunta ’yan daudu da masu sauya jinsi.

A shekara ta 2007 ne majalisar dokokin kasar ta Kuwait ta gyara dokar wadda a karkashinta duk wanda aka kama da laifi za a iya yi masa hukuncin daurin da ya kai na shekara daya da tara.

To amma hukuncin da kotun ta yanke a Larabar nan ya ce gyaran da aka yi wa dokar ya saba wa tsarin Mulki kamar yadda BBC ya ruwaito.

Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Amnesty International ta ce hukuncin gagarumar nasara ce ga ‘yancin masu neman jinsi daya da makamantansu a yankin Fasha.

Lynn Maalouf ta kungiyar a yankin Gabas ta Tsakiya ta yi kira da a gaggauta sakin Maha al-Mutairi, mai shekara 40, wani dan daudu da ya mayar da kansa mace, abin da ya sa aka daure shi tare da tara a karkashin dokar.