✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soma horas da ’yan sa-kai don kawo karshen ’yan bindiga a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle ya sha alwashin aiwatar da karin matakan yaki da ta’addanci a jiharsa.

Gwamnatin Zamfara ta kaddamar da shirin horas da sabbin jami’an tsaron sa-kai da ta dauka domin dakile hare-haren ‘yan bindiga a karkashin kungiyar CPG a takaice.

Bayanai na nuni da cewa an zabo jami’an tsaron na CPG (Community Protection Guards) ne daga dukkanin masarautu 19 da ke fadin jihar.

Yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da aikin horas da sabbin jami’an tsaron a ranar Asabar, Gwamna Bello Matawalle ya sha alwashin aiwatar da karin matakan yaki da ta’addanci a jiharsa, la’akari da mummunan halin da ‘yan bindiga suka jefa dubban mutane musamman a yankunan karkara.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Zamfara ta sanar da yanke shawarar bai wa al’ummar jihar damar mallakar bindigogi domin kare kansu daga ta’addancin ‘yan bindiga.

Zamfara da ke kan gaba a tsakanin jihohin Arewacin Najeriya masu fama da hare-haren ’yan bindiga, a baya mahukuntan jihar sun sha yunkurin kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’addan, amma lamarin ya ci tura.