✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soma shari’ar matashin da ya yi sanadiyar yanke kafar daliba

Mun samu wani bayanin sirri cewa yaron ya samu gurbin karatu a kasar waje.

An soma shari’ar matashin nan dan shekara 18 mai suna Aliyu Sanusi Umar, wanda ya yi sanadin yanke kafar wata daliba ’yar shekara 16 Fatima Sulaiman.

Shari’ar dai ta dauki hankalin jama’a sobada ana ganin kamar ana sako sako da lamarin musamman duba da fitowar da aka yi kotu a baya wadda ba a yi zaman shari’ar ba.

Aminiya ta ruwaito cewa makonni uku da suka gabata ne Fatima Sulaiman ta rasa kafarta sanadiyyar bige ta da mota da matashin ya yi, lokacin da suke murnar kammala jarrabawar NECO, lamarin da ya yi sanadiyar yanke kafarta.

Fatima ta ce yaron ba dan makarantar su bane kuma daga farko sai da aka kore shi da ya shigo makarantar inda daliban ke wasan murnar kammala jarabawa.

A zaman kotun dai lauya mai kare wanda ake zargi, Jacob Ochidi SAN, ya nemi bukatar bayar da yaron beli domin a cewarsa laifukan da ake tuhumarsa ba manyan laifukan da ba a da bayar beli ba ne.

“Doka tace ana bayar da beli ga laifukan da ba manyan laifuka sai in akwai wasu kwararan dalilai na kin bayar da shi.

“Kuma a wannan shari’ar babu dalilan da ka iya hana a bayar da shi beli, muna tausaya wa yarinyar da iyayenta akan yanayin da suka shiga, dukan mu ‘yan Adam muke abinda ya faru abin tausayi ne don haka muke tausaya wa iyayenta.”

Muryar Amurka ta ruwaito lauyan masu shigar da kara, Jamilu Malami, ya kalubakanci wannan bukatar da lauyan wanda ake zargi ya gabatar a zaman kotun.

Ya ce, “lauyoyin yaron sun shigar da bukatar beli amma dai bangaren gwamnati da bangaren yarinyar sun ki aminta, domin sun samu wani bayanin sirri cewa yaron ya samu gurbin karatu a kasar waje don haka akwai yiwuwar zai iya barin kasar nan kowane lokaci.

“Sannan kuma akwai yiwuwar cewa ko don lafiyar shi ya kamata a bar shi gidan gyaran hali har kura ta kwanta.”

Alkaliyar kotun majistire, Mariya Haruna Dogon Daji, ta dage zaman zuwa 8 ga wannan wata don yanke hukunci a kan bayar da belin ko akasin haka.

Yadda matashin ya raba ni da kafata  —Fatima

A ranar Alhamis 25 ga watan Agusta ne Aliyu Sanusi Umar ya take kafar Fatima Suleiman a lokacin da yake wasa da mota, lamarin da ya yi sanadiyyar yanke kafarta ta dama.

Lamarin ya jefa mutane cikin alhini da jimami, kasancewar abin da ya faru da dalibar mai shekaru kasa da 20 a ranar da ta kammala sakandare.

Aminiya ta ziyarci buduwar a gadonnta na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo domin jin yadda lamarin ya faru.

Fatima Suleiman ta shaida wa Aminiya cewa, “A ranar Alhamis bayan kammala jarrawabarmu ta NECO a makarantar Khalipha International School, sai muka fito waje saboda a cikin makaranta ana wasa da ruwa don murnar kare makaranta.

“Bayan na kira mamata kan ta zo ta dauke ni, muna a zaune a gefen makaranta ni da kawayena biyu, sai wani dalibi ya zo da abokansa, inda wand ya take ni da motar ba dan makarantar ba ne, yana tare da ’yan makarantar ne suna wasa da mota, suna gudu.

“Lokacin da ya tun karo ni ina zaune kafin na tashi sai ya taka kafata ya wuce, hankalina bai gushe ba har aka kawo ni asibiti aka yanke kafata.”

‘Ba zan iya yafe masa ba’

Dalibar ta ce, ba za ta iya yafe wa wanda ya raba ta da kafarta ba, saboda ya riga ya yi wa rayuwata illa, ya raba ni da kafa daya.

Ina neman taimako a gyara min kafata, don in ci gaba da rayuwa kamar kowa. Ina rokon Gwamnatin Jihar Sakkwato ta taimaka wa lafiyata a kuma hukunta wanda ya yi min haka,” inji ta.

Ina son na zama likita

Game da batun ci gaba da karatu kuwa, Fatima Suleiman ta ce, “Insha Allah zan ci gaba har sai na cim ma burina na zama cikakkiyar likita, domin taimaka wa al’ummata.

“Ina son a taimaki rayuwata, ya kamata iyaye su rika kula da yaransu a wannan zamani.”

Dangane da yadda take ji a yanzu cikin hawaye Fatima ta ce, “Ina cikin damuwa gaskiya domin ban saba da irin wannan rayuwar ba, amma na yi tawakkali domin kaddarar Allah ce ba wanda ya isa ya hana faruwar haka.

Ni da duk wanda zai samu kaddara irin haka kawai a yi hakuri a dauki kaddarar, abin da ya faru, ni na bar wa Allah komai.”

Mahaifiyarta Hajiya Hadiza Suleiman ta ce, ba abin da yake damun ta shi ne in ta dubi ’yar tata sai ta ga kamar an rusa makomarta.

“Abin yana ci mani rai safe da rana a zaune nake kwana tun sa’ar da abin nan ya faru. Muna neman a kwato mana hakkinmu.

“’Yata ta rasa kafa kuma ba yadda za a yi a sake dawo da kafarta, sannan abin da ya faru ba hadari ba.

“Ya kamata daga kan Fatima wani yaro ba zai sake gangaci da mota ba. A biya diyya ga ’yata.

“Ina kira ga gwamnati don Allah ta shiga cikin lamarin nan ta kwato mana hakkinmu don ya zama darasi ga iyayen da suke barin ’ya’yansu na tuka mota ba fasali a cikin gari, suna salwantar da rayukan mutane,” inji ta.

Mahaifin yarinyar Suleiman Boyi ya ce, “Gaskiya na samu bacin rai kwarai da gaske, a lokacin da abin ya faru. Da aka sanar da ni, na dauka karaya ce ta samu kafarta.

“Domin ita da kanta ta kira ni bayan abin ya faru, sai daga baya ne na fahimci abin ya wuce karaya, kafa ce ta fita gaba daya.”