✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tallafa wa wadanda ambaliya ta shafa a Adamawa

Kimanin gundumomi 11 da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa da kuma ‘yan gudun hijira a Jihar Adamawa ne suka samu tallafi daga Hukumar Raya Yankin…

Kimanin gundumomi 11 da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa da kuma ‘yan gudun hijira a Jihar Adamawa ne suka samu tallafi daga Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC).

Da yake bayar da tallafin ga ‘yan gudun hijirar da ke sansanin Malkohi na Karamar Hukumar Yola ta Kudu, mataimakin manajan daraktan NEDC, Farfesa Bobboi Umar, ya ce sun tallafa wa sama da mutum 100 a sanasanin.

“Mun raba tallafin kayan abinci na miliyoyin Nairori ga mazauna wannan sansani”, inji shi.

Ya kuma ce NEDC za ta fadada rabon tallafin ga karin wasu mutanen da ke wasu sansanonin gudun hijira a yankin.

Kazalika, hukumar ta raba kayayyaki ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a sassan jihar.

Farfesa Bobbi ya ce hukumar na raba tallafin ne domin rage radadin iftila’in ga al’ummar jihar.

Da yake mayar da jawabi a madadin gwamnatin jihrar, Babban Sakataren hukumar agaji ta jihar (ADSEMA), Mohammed Sulaiman ya yaba wa hukumar saboda bayar da tallafin.