✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tashi da azumin watan Ramadan a Najeriya

Galibin Musulmin Najeriya sun bi sahun takwarorinsu a wasu sassan duniya wajen tashi da azumin watan Ramadan na bana. Hakan dai ya biyo bayan sanarwar…

Galibin Musulmin Najeriya sun bi sahun takwarorinsu a wasu sassan duniya wajen tashi da azumin watan Ramadan na bana.

Hakan dai ya biyo bayan sanarwar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayar da maraicen Alhamis cewa an ga wata a wasu sassan kasar.

Sarkin Musulmin ya ce an samu labarin ganin watan ne daga shugabannin addini da kungiyoyi daban-daban a Nijeriya.

Sai dai kuma bai zayyano garuruwan da aka ga watan ba, amma ya ce kwamitin ganin wata ya tantance sahihancin duk bayanan da aka samu kafin a kawo maganar gaban shi.

Hakan dai na nufin Juma’a 24 ga watan Afrilu 2020 ta zama 1 ga watan Ramadan 1441.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya roki Musulmi su yaiwata addu’a a cikin wannan watan Allah Ya kawo karshen annobar coronavirus.

“Ina kira ga mutane su bi umarnin da jami’an lafiya da gwamnatoci suka sanya kan kare kamuwa da cutar coronaviru”, inji shi.

Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga masu wadata su taimaki talakawa a watan Ramadana ba tare da kula da bambancin siyasa da kabila ba.