✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tono gawar mamallakin dogon benen da ya rushe a Legas cikin baraguzai

An tono gawar ne da almurun ranar Alhamis daga cikin baraguzai.

Kimanin kwana uku bayan dogon benen nan mai hawa 21 ya rushe tare da danne mutane a unguwar Ikoyin Jihar Legas, a ranar Alhamis an tono gawar mamallakinsa, Femi Osibona, a cikin baraguzai.

Marigayin dai shi ne Shugaban kamfanin Fourscore Homes Limited, wanda yake aikin gina benen.

Masu Aikin ceto wadanda suka zanta da Aminiya sun ce an tono gawar tasa ne daga cikin baraguzai da almurun Alhamis.

An dai ta shaci-fadi akan inda marigayin ya shiga, tun bayan rushewar ginin.

Ya zuwa yanzu dai, kimanin mutum tara ne aka ceto a raye, yayin da 30 kuma aka tabbatar da rasuwarsu.

A ranar Talata ne aka tono gawar hadimin Osibona, shi ma daga cikin ginin.