✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsamo gawar mutum 14 da suka nutse a ruwa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja

Ana ci gaba da bincike mutanen da suka nutse a cikin ruwan.

Akalla gawar mutum 14 aka samu a ruwan Zumba-Guni da ke Jihar Neja, bayan wani hatsarin jirgin ruwa da ya rutsa da wasu mutane da suka tsere wa harin ‘yan bindiga a jihar.

Wani mazaunin yankin mai suna Micheal Madaki, ya shaida wa Aminiya cewa zuwa yanzu an samu gawar yara hudu da mata 10, a yayin da gwanayen linkaya ke ci gaba da binciken sauran wadanda suka nutse a ruwan.

Kazalika, gwamnan Jihar Abubakar Sani Bello ya bai wa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA), umarnin gaggauta ceto mutanen da hatsarin ya rutsa da su.

Gwamnan ya bada umarnin ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnatin Jihar ta fitar, Mary Noel-Berje, inda ya bayyana lamarin a takaicinsa kan aukuwar lamarin.

Hatsarin dai ya faru ne sakamakon tsere wa harin ‘yan bindiga da mazauna yankun suka yi, lamarin da ya kai ga salwantar rayukan mutanen da ba a san adadinsu ba kawo yanzu.