✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsare mutum biyu bisa zargin kashe Tolulope

Abokan hafsar soji ta farko mai tuka jirgin saman yaki ne suka kade ta da mota.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tsare wasu mutum biyu da take zargi da hannu a mutuwar Tolulope Arotile mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a kasar.

Kakakin rundunar Ibikunle Daramola ya ce ta fara bincike kan mutuwar hafsar sojin saman kuma za ta sanar da jama’a duk abun da ya kamata su sani game da mutuwarta.

Rundunar ta ce abokin karatun Tulolope na makarantar sakandare ne ya kade ta da mota ya ce “Yanzu haka yara biyun da ke motar na hannu kuma ana bincike a kansu.

Ya ce abun ya faru ne a lokacin da abokin karatun marigayiyar ya tuko mota da baya a kokarinsa na gaisawa da ita, bayan ya ango ta.

“Da fari na fidda sanarwar rasuwar ta inda na ce ta rasu ne sakamakon hatsari akan hanya.

“Daga baya na sanar cewa abokin karatun ta na sakandare ne ya kade ta da mota a lokacin da ya hange ta, cikin shauki da rawar jiki ya yiwo baya da zummar gaisawa da ita.

“Lamarin ya faru ne a cikin Barikin Sojin Sama don haka daga nan ne za a faro binciken, za kuma a sanar da jama’a abun da ya kamata su sani”, inji shi.

Rundunar ta ce za a binne marigayiyar a Makabartar Sojoji ta Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis mai zuwa, 23 ga watan Yuli.

Marigayiya Tolulope Arotile ‘yar asalin jihar Kogi ta rasu ne a ranar Talata, 14 ga watan Julin 2020.