✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare shanu 44 a Bayelsa saboda karya dokar hana kiwo ta Jihar

Sai dai iya shanun aka kama, ban da makiyayan.

Kwamitin kar-ta-kwana kan tabbatar da dokar hana kiwo a Jihar Bayelsa ya kama shanu kimanin 44 da ke gararamba a Yenagoa, babban birnin Jihar.

Kwamitin, wanda Kwamishinan Noma da Ma’adinan Gargajiya na Jihar, Mista David Alagoa, ke jagoranta, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro ne dai ya kama shanun daga hannun makiyayansu.

Aminiya ta gano cewa iya shanun kawai aka kama, ban da masu kiwonsu, ko mamallakansu.

Ko a watan da ya gabata dai, sai da kwamitin kula da albarkatun gona na Jihar ya gurfanar da wasu makiyaya guda su a gaban kotu bisa karya dokar hana kiwon.

Manoma a Jihar dai na korafin cewa makiyayan na yi musu ta’adi a gonaki, inda suka roki Gwamnatin Jihar da ta tabbatar dokar na aiki yadda ya kamata don a gujewa tashin-tashina.

Jihar Bayelsa dai kamar sauran takwarorinta na Kudancin Najeriya ta sanya dokar haramta kiwo a fili a fadin Jihar.