✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare shugaban adawar Tanzaniya

Jami’an tsaro sun cafke shugaban jam’iyyar Chadema ta kasar Tanzaniya, Freeman Mbowe.

Jami’an tsaro sun cafke shugaban babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzaniya, wato Chadema, Mista Freeman Mbowe.

A cikin tsakar dare ne jami’an tsaro suka kai wa Mbowe da wasu shugabannin jam’iyyarsa 10 samame a yayin da suke shirin taron neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

An cafke Mista Mbowe ne wata hudu bayan Shugabar Kasar mace ta farko, Samia Suluhu Hassan ta fara mulki a watan Maris bayan rasuwar Shugaba John Magufuli.

Chadema ta ce, “Tir da wannan murkushe ’yancin bayyana ra’ayi. Wannan ai alama ce ta ci gaban salon mulkin kama-karya na Shugaba John Magufuli.

“’Yan sanda sun bi sawun Freeman Mbowe har zuwa otal din da yake da misalin 02:30 na dare suka tsare shi tare da wasu shugabannin jam’iyyar,” a birnin Mwanza, mai tashar jirgin ruwa, inji jam’iyyar.

Hukumomin birnin sun yi kamen ne bayan Mbowe ya lashi takobin gudanar da taron neman sauya tsarin mulkin kasar,  duk da cewa hukumomi sun hana taron saboda dokar COVID-19.

A wani bidiyo, an ga madugun adawan na cewa, “Ba za mu ci gaba da bin tsohon tsari ba.

“Muna da ’yancin amma an kama mu, an buge mu, ana zargin mu, an kai mu kotu tsawon shekaru biyu zuwa uku sannan a sake mu.

“Idan suna so su kame dukkan mambobin jam’iyyar Chadema, to su fara fadada gidajen yarin saboda dukkanmu a shirye muke da a kama mu kuma ba za mu nemi beli ba.”

A halin yanzu dai an kai ragowar ’yan jam’iyyar ta Chadema ofishin ’yan sanda a birnin na Mwanza, amma babu bayani kan inda Mista Mbowe yake.

“Muna so ’yan sanda su fito su bayyana inda suka kai shugabanmu da kuma dalilinsu na tsare shi,” a cewar Chadema.