✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare Usman Bugaje saboda sukar Gwamnatin Buhari

Jami’an tsaro sun tsare tsohon Sakataren rusasshiyar jam’iyyar AC, Dokta Usman Bugaje, saboda sukar kamun ludayin Gwamnatin Buhari kan sha’anin tsaro a Najeriya. ’Yan sandan…

Jami’an tsaro sun tsare tsohon Sakataren rusasshiyar jam’iyyar AC, Dokta Usman Bugaje, saboda sukar kamun ludayin Gwamnatin Buhari kan sha’anin tsaro a Najeriya.

’Yan sandan ciki sun gayyaci Usman Bugaje zuwa ofishinsu ne bayan wata hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT a ranar Laraba.

An gano cewa wani sashe na Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa ne ya yi wa Dokta Bugaje tambayoyi kafin daga baya aka bar shi ya tafi.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin hukumar tsaro ta DSS, Peter Afunanya, domin samun karin bayani, amma ya turo da rubutaccen sako cewa yana halartar wani taro.