✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsaurara tsaro gabanin zuwan Buhari Yola

Buhari zai ziyarci birnin Yola a ranar Juma'a.

Yanzu haka an tsaurara matakan tsaro dangane da ziyarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai Yola, babban birnin Jihar Adamawa a ranar Juma’a.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Suleiman Nguroje ya fitar ranar Alhamis a birnin Yola.

DSP Nguroje ya shawarci jami’an ’yan sandan da aka tanada domin tsaurara matakan tsaro saboda zuwan shugaban kasar da su nuna kwarewa wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Rundunar ta shirya tura dakarunta domin sa ido da kuma kara karfin gwiwa wajen gudanar da aikin sintiri domin tabbatar da an kiyaye doka da oda.

“Rundunar ta kuma tanadi karin kayan aiki da kwararrun ’yan sanda da suka hada da jami’an ko-ta-kwana da masu yaki da ta’addanci da kwantar da tarzoma da kuma masu kula da cunkoson jama’a da ababen hawa,” a cewarsa.

Ya ce rundunar ’yan sandan za ta yi aikin hadin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da kiyaye doka yayin ziyarar shugaban kasar.

Nguroje ya kuma nemi jama’a da su bai wa jami’an tsaro hadin kai domin sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya rataya musu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Buhari zai ziyarci birnin Yola ne domin jajanta wa al’ummar Jihar Adamawa dangane da rasuwar Ahmed Joda, Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Alhaji Ahmed Joda, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Shirye-Shiryen Mika Mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata.