✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsawaita lokacin aikin Keke NAPEP a Yobe

Gwamnatin Yobe ta tsawaita lokacin aikin masu sana'ar haya da Keke NAPEP zuwa karfe 8 na dare

Gwamnatin Yobe ta tsawaita lokacin aikin masu sana’ar haya da babur mai kafa uku (Keke NAPEP) zuwa karfe 8 na dare a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa sassaucin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 4 ga watan Maris da muke ciki a daukacin kananan hukumomi 17 da ke Jihar Yobe.

Sanarwar da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Birgediya Dahiru Abdulsalam (murabus), ta ce gwamnatin ta yi haka ne saboda an samu ingantuwar sha’anin tsaro a fadin jihar.

Bugu da kari matafiya na shan wahala saboda takaita zirga-zirgar Keke NAPEP daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma da aka yi a baya.

A cewar sanarwar “Gwamnatin Jihar Yobe ta yi nazari kan yanayin tsaro a fadin kananan hukumomin jihar 17 inda ta lura da yadda lamarin tsaro ya inganta a fadin jihar baki daya.

“Bayan haka, gwamnati ta lura da irin wahalhalun da matafiya ke fuskanta sakamakon kayyade lokacin da aka yi a baya wato daga karfe 6:00 na safiya zuwa karfe 6.00pm na yammaci na yin amfani da babur masu taya  uku na kasuwanci (KEKE NAPEP).

“Saboda haka, Gwamnan Mai Mala Buni ya amince da sake duba sa’o’in aiki ga masu haya da Keke NAPEP.

“Saboda haka, an umurce ni da in sanar da cewa a halin yanzu lokacin aikin masu Keke NAPEP ya koma daga karfe 6:00 na safiya zuwa 8:00 na yamma a kullum daga ranar Juma’a 3 ga Maris, 2023.

“Saboda haka, Gwamnan Jihar Yobe ya umarci dukkan hukumomin tsaro a jihar da su tabbatar da bin wannan umarnin.

“Hakazalika, ana bukatar shugabannin kungiyar masu babura ta kasa (NACTOMORAS) reshen jihar Yobe da su yi taka-tsan-tsan tare da bayar da cikakken hadin kai wajen aiwatarwa da bin wannan umarni.