✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsige Omehia daga matsayin tsohon Gwamnan Ribas

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta umarci Celestine Omehia ya dawo da hakkokin da aka biya shi daga 2015 zuwa yanzu

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta tsige Celestine Omehia daga matsayinsa na tsoffin gwamnan jihar.

Majalisar ta soke duk wasu hakkoki da alfarmar tsohon gwamna da Omehia ke samu, sannan ta umarce shi ya dawo wadanda gwamnatin jihar ta biya shi daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Majalisar ta dauki matakin ne a ranar Alhamis, baya Shugaban Masu Rinjaye, Martin Amaewmule ya bukaci janye matakin da ta dauka a 2015 na ayyana Sir Omehia a matsayin tsohon gwamnan jihar.

Matakin na 2015 ya tilasta wa bangaren zartaswa da Gwamna Nyesom Wike daukar Omehia a matsayin tsohon Gwamnan Jihar Ribas tare da ba shi duk wata alfarma da hakkokin da tsoffin gwamnonin jihar ke samu.

A shekarar 2015 ne, bayan cin zaben Wike ya ba da umarnin daukar Sir Omehia a matsayin tsohon gwamnan jibas, duk kuwa da umarnin Kotun Koli na 2007 da ya soke zaben sa.

Kotun Kolin ta ce doka ba ta san da Omehia a matsayin tsohon gwamnan Ribas ba, duk kuwa da cewa ya mulki  jihar na tsawon wata biyar.

Bayan Wike ya yi gaban kansa wajen ayyana shi a matsayin tsohon gwamnan ne ya mika wa Majalisar kudirin, ta amince da ita.

A baya-bayan nan ne dangantaka ta yi tsami tsakaninsu saboda Omehia na goyon bayan  bangaren dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubarkar.

Mike da Atiku na takun saka tun bayan zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, wanda Wike ya zo na biyu.