✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato

An maye gurbinsa da Honorabul Sanda Yakubu.

Majalisar Dokokin Jihar Filato ta tsige shugabanta, Honorabul Abok Ayuba Nuhu, a safiyar Alhamis.

An tsige Shugaban Majalisar ce a zaman da Shugaban Masu Rinjayen Majalisar ya jagoranta.

A zaman na safiyar Alhamis, mutum 16 daga cikin mambobin majalisar 24 sun kada kuri’ar amincewa da tsige Honorabul Abok.

Majalisar ta kuma maye gurbinsa da Honorabul Sanda Yakubu, daga mazabar Karamar Hukumar Bassa.