✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar Babban Limami a cikin mota

An tsinci gawar wani Babban Limami da ke unguwar Atiba da ke garin Ijebu-Ode na Jihar Ogun state, Sheikh Mushafau Bakare a cikin motarsa. An…

An tsinci gawar wani Babban Limami da ke unguwar Atiba da ke garin Ijebu-Ode na Jihar Ogun state, Sheikh Mushafau Bakare a cikin motarsa.

An gano gawar Sheikh Mashafau ne bayan bacewarsa a ranar Laraba, har aka yi ta neman shi.

Daga baya aka tsinci gawarsa a cikin sabuwar motarsa kirar Toyota Highlander da safiyar Alhamis a unguwar Ikangba da ke Karamar Hukuamr Odogbolu ta Jihar.

’Yan sansda ne suka tsinci gawar babban limamin mai shekara 60 da ’yan kai, amma wasu na zargin an yi garkuwa da shi ne sannan aka kashe shi.

Amma kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce “Babu wata alamar da ke nuna an yi amfani da karfi a jikin gawar babban limamin, an dai tsinci gawarsa ce a cikin motarsa.

“Babu wani abu da ke nuna alamar ’yan bindiga ko masu garkuwa a cikin wannan lamari.

“Babban Limamin ya bar gida ne domin ya zagaya gari, amma da bai dawo gida a kan lokaci ba sai iyalansa suka rika kiran wayarsa, da ba su ji an dauka ba sai suka sanar da ’yan sanda.”

Ya ce bayan ’yan sanda sun yi yawon sintiri ne suka gano gawarsa a cikin mota.

“Binciken da muka gudanar ya nuna yana fama da hawan jini, kuma abin ya taso masa a lokacin da babu wani wanda zai taimaka masa.

“Amma babu wata alamar an yi masa amfani da karfi a jikin gawar tasa.”

Tuni dai aka binne gawar malamin a ranar Alhamis.