✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar daliban jami’ar Kwara 2 tsirara a daki

An tsinci gawarsu ne lokacin da ake tsaka da jarrabawa

An tsinci gawar wani daliban Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Tobiloba Daniel, da wacce ake zargin budurwarsa ce, Arewa Abayomi, tsirara a wani dakin kwanan dalibai da ke kusa da jami’ar.

Duka mutum biyun dai ’yan aji biyu ne a jami’ar, kuma suna cikin masu rubuta jarrabawar da yanzu haka ake yi a jami’ar.

Wani dalibi a jami’ar, ya shaida wa Aminiya cewa, “Muna tunanin masoya ne, kuma mun damu sosai lokacin da muka ga ba mu gan su a dakin jarrabawa ba na tsawon kwana uku.

“Sai bayan abokansu sun ziyarci dakunansu ne a inda suke zama a wajen makaranta sannan aka tsinci gawar su tsirara. Mun fi zargin cewa rasuwar tasu na da alaka da ta’ammali da guba,” inji dalibin.

Kakakin jami’ar, Hajia Saeedat Aliyu, ta ce har yanzu babu wata sanarwa a hukumance a kan batun.

Sai dai Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da labarin, inda ya ce, “bayanin da muka samu shi ne an tsinci gawarsu a cikin dakin, inda aka sanar da ’yan sanda.

“Jami’anmu sun balle kofar sannan aka kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH) don yin bincike a kan musabbabin rasuwar tasu.”