✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar karuwa a dakin Otal a Delta

An tsinci gawar wata kilaki a dakinta a wani Otal da ke jihar Delta bayan an soke ta da wuka, an kuma makure ta har…

An tsinci gawar wata kilaki a dakinta a wani Otal da ke jihar Delta bayan an soke ta da wuka, an kuma makure ta har ta rasa ranta.

Lamarin ya faru ne a wani fitaccen Otal da ke garin Ughelli na karamar hukumar Ugheli ta Arewa da ke jihar.

Matar, wacce ake kira da Misis Confidence mai zaman kanta, an gano gawar tata ne bayan da abokan sana’arta suka ji ta shiru a daki na tsawon wani lokaci ba ta fito ba sai suka shiga cikin zullumi.

Da suka yi ta buga kofarta suka ji shiru, sai suka kutsa kai a inda suka sami gawarta a kwance da raunin da aka yi mata na suka da wuka da kuma makureta.

Wannan ya sa abokan sana’ar suka watse, yayin da mutuwarta ta haddasa tsoro da firgici a tsakaninsu da kuma sauran mutanen unguwar da abin ya faru.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya kuma tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa “an soketa ne da wuka a ciki, sannan aka makure ta har ta mutu”.

Ya kuma ci gaba da cewa, har yanzu ba su kama kowa ba, amma suna ci gaba da bincike kan lamarin.