✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar magidanci a bakin rafi a Sanga

An tsinci gawar wani magidanci mai kimanin shekara 65 mai suna Danjuma Bako yashe a bakin rafi a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.…

An tsinci gawar wani magidanci mai kimanin shekara 65 mai suna Danjuma Bako yashe a bakin rafi a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.

Magidancin, dan asalin kauyen Kiban da ke gundumar Gwantu, an ce ya halarci wata jana’iza ne na wani dan uwansa da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi daga gonarsa, amma daga nan ba a kara jin duriyarsa ba.

Bayan jiran tsammani da danginsa suka yi ne washegari ranar Litinin suka fita nemansa, inda suka ci karo da gawarsa kasa ta rufe gefen jikinsa a bakin rafi.

Wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce wanda marigayin ya je jana’izarsa wasu mahara ne suka kashe shi a Unguwan Anjo da ke karamar hukumar Jama’a mai makwabtaka da su.

Yayin da Aminiya ta tuntubi shugaban karamar hukumar Sanga, Mista Charles Danladi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana damuwarsa kan karuwar kashe-kashe a yankin.

Mista Danladi ya ce dole sai jami’an tsaro sun tashi tsaye don ganin sun shawo kan wannan matsalar da taki ci ta ki cinyewa.

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa a kwanan nan ma wasu matasa sun kama wata yarinya ‘yar kauyen Anka amma mazauniyar Abuja bayan ta kawo ziyara ga fitaccen dan siyasar yankin, Sr Ishaya Abu Anka suka yi mata fyade.