✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar wata mata a cikin Otel a Filato

ASP Gabriel ya ce a halin yanzu bincike ya kan kama.

An yi kacibus da gawar wata mata a wani Otel mai suna Domus Pacis Guest House da ke kan titin Zariya a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

A cewar mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, an tsinci gawar matar ce jina-jina a daki mai lamba ta 302 da ke Otel din.

Ya ce bayan samun wannan mummunan rahoton ne Kwamishinan ’Yan sanda, CP Bartholomew Nnamdi Onyeka ya bayar da umarnin cewa jami’an binciken kwakwaf da leken asiri na rundunar su dauki hotunan gawar matar sannan kuma mika a zuwa dakin ajiye gawawwaki domin bin diddigi ta hanyar amfani da kimiyya da fasahar zamani.

ASP Gabriel ya ce a halin yanzu bincike ya kan kama domin gano duk wasu dalilai dangane da yadda matar ta riga mu gidan gaskiya domin cafke masu hannu a wannan aika-aika.

Kazalika, ya ce Kwamishinan ’yan sandan ya jagoranci wani taron gaggawa da dukkan masu otel-otel a jihar inda ya yi musu karin haske kan wasu dabaru da hanyoyi na tsaro da za su magance aukuwar makamancin wannan lamari a lokuta na gaba.