✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar wata mata a otel a Zariya

Otel din da ma ya yi kaurin suna wajen kasancewa matattarar mata masu zaman kansu.

A tsinto gawar wata mata da ke sana’ar karuwanci mai suna Blessing John a dakin wani otel da ke garin Zariya a Jihar Kaduna.

Bayanai na cewa matar ta mutu ne sakamakon yankan rago da ake zargin wani da ya biya bukatarsa da ita ya yi mata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Blessing wadda ’yar asalin Jihar Binuwai ce ta zo garin Zariya ne kimanin makonni uku da suka gabata domin sana’ar karuwanci.

Marigayiya Blessing ta kama daki ne a wani otel da ya dauke da dakuna kusan 40, kuma ya kasance sansanin mata masu zaman kansu a titin Benin da ke Sabon garin Zariya.

Otel din da ma ya yi kaurin suna wajen kasancewa matattarar mata masu zaman kansu da kuma shaye shayen kayan maye.

Wani makwabcin otel din da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa an gano gawar Blessing ce sakamakon wani wari da aka rika ji yana fitowa daga dakinta.

Dalilin haka ya sa manajan otel din ya sanar da ’yan sanda kuma daga bisani aka balle kofar dakinta, inda aka riski gawarta jina-jina sakamakon yanka a wuyanta.

Lamarin ya ta da hankalin jama’a inda daga nan ’yan sandan suka garzaya da gawarta zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.

Majiyar ta kuma tabbatar wa wakilinmu cewa, shi ma manajan otel din tuni ’yan sanda suka gayyace shi a kokarinsu na gudanar da bincike.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Kaduna Mohammed Jalige, sai dai bai amsa kiran wayarsa ba da sakonnin kar ta kwana da aike masa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.