✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinto zoben aure da ya shekara 17 da bacewa a ruwa

Zoben ya dade da bacewa, na yi mamakin yadda aka gano shi.

Wani mai ninkaya a Birtaniya ya tsinto wani zobe da ya shekara 17 da fadawa cikin wani kogi tare da bacewa.

Hukumar ’yan sandan yankin ta wallafa a shafinta cewa, wani mai ninkaya ya tsinto zoben wanda aka yi ittifakin ya shekara 17 da bacewa, da ke dauke da sunan Stephanie da Noel.

Mai zoben mai suna Nissen, ya cewa surukinsa ne ya fara ganin sanarwar, sannan ya fada masa abin da ke faruwa.

“Surukina ne ya kira ni ya ce, min ya ga wata sanarwa a wani shafi game da wani zobe, kuma ya tura min sannan ya tambaye ni ko nawa ne,” kamar yadda ya shaida wa tashar labarai ta CBC.

Nissen, ya ce zoben aurensa ya bace shekara 17 da suka wuce, kuma bai gan shi ba sai yanzu da aka gano shi.

“Zoben ya dade da bacewa, na yi mamakin yadda aka gano shi,” inji shi.

Ya ce lokacin da zoben ya bace bai ma sani ba, saboda a ranar da abin ya faru shi da abokansa sun halarci wani taro, sai bayan da ya dawo cikin mota ya gano zoben ya bace.

Ya ce, an dawo masa da zoben a daidai domin yanzu suke cika shekara 20 da aure da matarsa Stephanie, wanda hakan ya ce zai kayatar da su sosai.

“Na yi mamakin yadda tsawon shekara 17 zoben yana nan da kyansa, na dauka yadda ya dade a kasan ruwa tabo da duwatsu sun danne shi,” inji shi.