✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsohe layukan sadarwa a Sakkawato

An toshe layukan sadarwa a kananan hukumomi 14 daga cikin 23 na jihar.

An rufe layin sadarwa a 14 daga cikin kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato, a wani yunkuri na magance matsalar ’yan bindiga a Jihar.

Da yake sanar da daukar matakin, Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce kananan hukumomin da aka katse hanyoyin sadarwar su ne suka fi fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.

A jawabin nasa na ranar Litinin, Tambuwal ya bayyana cewa an samu amincewar Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, kan daukar matakin, duba da nasarar da aka samu bayan katse hanyoyin sadarwa a Jihar Zamfara, makwabciyar jihar ta Sakkwato.

Tambuwal ya ce, “Nasarar da sojoji suka samu a Zamfara ta tilasta wa ’yan bindiga tserewa suna shigowa Jihar Sakkwato,” shi ya sa aka toshe layukan sadarwa a kananan hukumomin da suka hada da Tangaza, Tureta, Isa, Rabah, Goronyo da Dange Shuni da sauransu.

Rufe layin sadarwa da sauran matakan da aka dauka a Zamfara, inda sojoji ke ci gaba da yi wa ’yan bindiga luguden wuta, ya sa bata-garin kutsawa zuwa wasu sassa na Jihar Sakkwato, suna garkuwa da mutane suna kashe wasu tare da satar kayan abinci.

A Jihar Katsina, wadda ita ma makwabciyar Jihar Zamfara ce, an katse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 13 sakamakon matsalar tsaron da ta yi kamari, inda ’yan bindiga suka yi garkuwa da dururwan mutane.

Yankunan da aka katse layukan sadarwa a jihar sun hada da guda 10 wadanda Dajin Rugu — matattarar ’yan bindiga — ya ratsa ta cikinsu, da wasu uku da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Kaduna, wadda ita ma bata-garin sun addabe ta.

Jihohin Katsina da Zamfara, masu makwabtaka da Jihar Sakkwato sun kuma rufe kasuwannin mako-mako tare da takaita wasu harkoki, ciki har da jigilar dabbobi da ta itace da ma takaita sayar da man fetur.