✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura dalibin da ake tuhuma da cin zarafin Aisha Buhari gidan yari

Aisha Buhari ta fusata kan yadda dalibin ya ce ta ci kudin talakawa ta yi bulbul.

Kotu ta bai wa gidan yari ajiyar Aminu Mohammed, wani dalibin jami’a wanda Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari ke zargi da wallafa wasu sakonni na cin zarafinta a shafinsa na Twitter.

Idan ba a manta ba, an ruwaito cewar jami’an tsaro ne suka dauki Aminu, dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse, a Jihar Jigawa kan wasu kalaman batanci da ake zarginsa da yi wa Uwargidan Shugaban Kasar.

Rahotanni na cewa, uwargidan shugaban ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin dauko mata Aminu Adamu daga Jami’ar ta Jigawa bayan ya wallafa wasu kalamai a kanta, inda yake cewa, “Su mama an ci kudin talakawa an koshi”.

An bayyana cewar an gurfanar da Aminu ne a ranar Talata a gaban Babbar Kotun Tarayya mai lamba 14 a Abuja.

Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Mista Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a ba da Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

”Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci ’yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.”

“Akan haka muka bukaci kotun ta ba da shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba.

“Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar ’yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,” in ji CK Agu.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai ya ce “yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar ba da shi beli.”

A cewar kawunsa, Shehu Baba-Azare, rundunar ‘yan sandan ba ta sanar da ‘yan uwansa game da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Baba-Azare ya ce “A asirce aka gurfanar da shi a kotu, ba su sanar da mu ba, mun damu matuka da halin da yake ciki.

“Zai yi jarrabawar karshe a ranar 5 ga Disamba,” in ji Baba-Azare.

Tuni dai dubban mutane suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari wanda ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.