✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura dan sandan da ya kashe lauya gidan yari

Dan sandan ya harbi lauyar a ranar Kirsimeti.

Wata kotun majistare da ke yankin Yaba a Jihar Legas ta aike da Drambi Vandi, dan sanda da ake zargi da kashe wata lauya, Bolanle Raheem, a ranar Kirsimeti zuwa gidan yari.

An gurfanar da Vandi a gaban kotun da safiyar ranar Juma’a kuma za a ci gaba da tsare shi zuwa ranar 30 ga watan Janairu, 2023, lokacin da Ofishin Hukumar Shigar da Kara na Jihar Legas zai kammala bincike kan lamarin.

“An gurfanar da Vandi a kotu da safiyar nan kuma za a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Ikoyi har zuwa ranar 30 ga wtan Janairu, 2023,” in ji kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ta shafinsa na Twitter.

A ranar Alhamis ne Hukumar ’Yan Sanda ta dakatar da dan sandan da ake zargi ya hallaka lauyar daga aiki.

Hukumar ta kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin kafin ta dauki matakin da ya dace a kan jami’in.

Shi ma Kwamishinan ’Yan Sandan Legas, ya bukaci a bai wa ’yan sanda horo kan yadda za su kula da makamansu.

Barista Bolanle Raheem ta rasa ranta ne sakamakon harbin ta da dan sandan ya yi a ranar Kirsimeti, lokacin da suke kan hanyar komawarsu gida ita da ’yan uwanta.