✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura tawagar bincike ta musamman kan kisan matafiya a Jos

Matakin ya biyo bayan kashe wasu matafiya 25 a ranar Asabar.

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, IGP Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin tura tawagar ’yan sanda ta musamman domin kaddamar da bincike kan kashe matafiya a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar ’yan sanda na kasa, Frank Mba, ta ce matakin ya biyo bayan kashe mutum 25 a harin wanda wasu bata-gari suka tare matafiya ranar Asabar.

Sanarwar ta ce Matakamakin Sufeton ’Yan sanda, DIG Sanusi N. Lemu ne zai jagoranci tawagar sannan kuma za ta kunshi jami’ai daga bangarorin bincike da dama na rundunar.

Kazalika an tura karin jami’an tsaron zuwa yankin Rukuba da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa domin kare sake afkuwar tashin hankalin.

IGP Usman ya ce ya zuwa yanzu an kama mutum 20 da zargin aikata kashe-kashen sannan an ceto mutum 33 da suka ji jikkata yayin harin.

Aminiya ta ruwaito cewa, maharan da ake zargi matasan kabilar Irigwe ne sun tare motocin matafiyan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Jihar Ondo bayan sun halaraci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a Jihar Bauchi.