✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An umarci Gwamnatin Tarayya ta biya Nnamdi Kanu diyyar Naira biliyan 1

An kuma umarci gwamnatin ta nemi gafara daga wurinsa.

Babbar kotun Jihar Abia ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya diyyar Naira biliyan daya tare da neman gafara daga jagoran haramtacciyar kungiyar aware ta Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu a kan sumamen da jami’an tsaro suka kai gidansa a watan Satumba a 2017.

Kotun ta riki cewa sumamen da aka kai wa Nnamdi Kanu gidansa keta masa hakki ne da kuma ’yancin da dokar kasa ta tanadar.

Jagoran ’yan awaren, wanda kuma yake fuskantar wata shari’ar a kan cin amanar kasa da ayyukan ta’addanci a wata babbar kotun a Abuja, lauyansa, Aloy Ejimakor tun a ranar 27 ga watan Agustan 2021 ya shigar da karar gwamnatin Najeriyar a gaban babbar kotun ta Abiya a kan harin da ya ce jami’an tsaro sun kai gidansa.

Kanu wanda kotu ta bayar da belinsa ya tsere daga kasar bayan farmakin da jami’an tsaro suka kai gidan nasa, an sake kama shi a watan Yuni na 2021 a ketare aka dawo da shi Najeriya.

A yayin zaman babbar kotun ta Jihar Abia a ranar Larabar nan Mai shari’a Benson Anya ya yanke hukuncin cewa gwamnatin Najeriya ta biya Kanu diyyar naira biliyan daya saboda lalata gidansa da ke garinsu Isiama Afaraukwu da aka yi, sannan kuma gwamnatin ta nemi gafara daga wurinsa.

Yayin da kotun ta Abia ke hukuncin, Nnamdi Kanun ya kuma bayyana a babbar kotun da ke yi masa shari’a a Abuja a yau inda Mai sharia’a Binta Nyako ta dage shar’ar tasa har zuwa 16 ga watan Fabrairu.