✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An wajabta wa ma’aikatan Ondo yin rigakafin COVID-19

Dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2021.

Gwamnatin Jihar Ondo ta wajabta yin allurar rigakafin COVID-19 ga ma’aikatan Jihar, ko kuma su daina zuwa wajen aikin.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar, Mista Segun Odusanya, a ranar Laraba a birnin Akure.

Ya ce daga ranar daya ga watan Nuwamban 2021, ya zama tilas ga ma’aikata a Jihar su fara nuna katin shaidar karbar allurar rigakafin kafin su shiga wuraren ayyukansu.

“Umarnin zai fara aiki daga daya ga Nuwamba kuma dole ne ma’aikata su ci gaba da bin matakan kariyar COVID-19 a Jihar nan,” inji sanarwar

Ya ce umarnin ya zama dole, biyo bayan yadda cutar ke ci gaba da barazana ga rayukan al’umma a Jihar.

Odusanya, ya ce an fitar da sabuwar dokar bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Jihar, kuma za ta fara aiki da karfinta daga ranbar daya ga watan.

Kazalika, ya ce wajabta dokar na nufin kare rayuwar ma’aikatan Jihar, ganin cewar cutar ba ta kare ba amma mutane na sakaci da ita.

Daga nan ya shawarci ma’aikatan da su kasance masu yin gwajin Hawan Jini, Ciwon Suga da sauran cututtuka don dakile su tun a matakin farko.

Odusanya, ya sake kira ga ma’aikata da su kasance masu jajircewa wajen gudanar da ayyukansu a fadin Jihar.