✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ware wa gyaran hanyar Kano-Maiduguri karin N8bn

An ware karin kudaden ne domin kammala fadada babbar hanyar mai nisan kilomita 560

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince a kashe karin Naira biliyan takwas a kan aikin gyaran titin da ya tashi daga Kano ya bi da Wudil zuwa Shuwarin.

Kudaden za su ba da damar ci gaba da fadada babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri mai ninsan kilomita 560 ta za mai hannu biyu.

Ministan Yada Labari da Raya Al’adu, Lai Mohammed ya ce zaman ya amince da bukatar “karin Naira biliyan takwas” wanda Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya gabatar.

Ya ce zaman wanda wanda Shugaba Buhari ya jagoranta ya kuma amcince da kashe Naira biliyan 22.25 domin gyaran sashe na biyu na hanyar da ta tashi daga Apapa-Oworonsoki-Ojota mai nisan kilomita 8.1.

“A 2018 gwamnati ta ba da wa kamfain Dangote aikin gyaran a kan biliyan N72, kuma lokacin wannan sashen na da kyau.

“Yayin da aikin na Oworonsoki ke ke zuwa karshe abin da ya fi dacewa shi ne a hada har da bangaren da bai samu matsala sosai ba”, inji ministan.

Sai dai ya yi bayani cewa “Kamfanin Dangote ne zai gina hanyar kuma za a ciri kudin ne a tsawon shekaru daga haranin da kamfanin zai biya gwamanti”.