✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yaba wa jami’an tsaro kan kashe ’yan bindiga a Abuja

Shugaban Karamar Hukumar Abaji a Abuja, Alhaji Abdulrahman Ajiya ya jinjinawa 'yan sanda da 'yan banga kan namijin kokari da suka yi wajen kashe 'yan…

Shugaban Karamar Hukumar Abaji a Abuja, Abdulrahman Ajiya ya jinjinawa ‘yan sanda da ‘yan banga kan kashe ’yan bindiga biyu da suka yi a yankin.

Hadin gwiwar ’yan sanda da ’yan banga sun yi nasarar hallaka ’yan bindigar ne a ranar Lahadi yayin da ’yan bindigar suka yi awon gaba wani mutum a yankin.

Ajiya, a yayin da yake ganawa da ’yan bangar yankin a ofishinsa, ya yaba musu kan irin kokari da suke yi na tabbatar da tsaro ganin ya samu a yankin.

Kazalika, ya jinjina wa Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya, Bala Ciroma da Ministar Birnin Tarayya, Ramatu Tijjani Aliyu kan yadda suke fadi-tashi wajen yaki da matsalar tsaro a Abuja.

Shugaban Karamar Hukumar, ya shawarci jama’ar yankin da su yi aiki kafada-da-kafada da jami’an tsaro wajen ba su bayanan sirri da za su taimaka wajen dakile matsalar garkuwa da mutane.