✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yaba wa sojojin suka ‘kashe ’yan Boko Haram 105’

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya ya yaba wa dakarunsa bisa nasarar da suka yi ta dakile wani hari da kungiyar Boko Haram ta kaddamar…

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya ya yaba wa dakarunsa bisa nasarar da suka yi ta dakile wani hari da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a kan kauyen Buni Gari na jihar Yobe ranar Asabar har suka kashe mayakanta 105.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya yaba wa dakarun na rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko haram ne a lokacin da ya kai ziyara Sansani na 3 na sojojin da ke Damaturu ranar Lahadi.

Babban hafsan ya kuma ziyarci wasu sojoji biyu da suka yi rauni yayin dauki ba dadin da aka yi da ma sauran sojojin da ke kwace a asibitin soji da ke Damaturu kafin ya wuce zuwa Makarantar Horar da Zaratan Sojoji da ke Buni Yadi.

Kwamandan Shiyya ta Biyu ta Rundunar, Birgediya Janar Lawrence Araba, wanda kamfanin dillancin labrai na NAN ya ruwaito yana yi wa Janar Buratai bayani, ya ce sojojin sun yi wannan nasara ne saboda wasu bayanan sirri da suka samu cewa ’yan kungiyar ta Boko Haram na shirin kai musu farmaki.

Hakan ne inji Janar Araba ya bai wa sojojin na Najeriya damar daukar mataki cikin gaggawa don dakile harin, lamarin da ya kai ga yin kazamar arangama da abokan gabar .

Ya kuma ce an san adadin mayakan Boko Haram din da aka kashe ne bayan da aka raraka su, sannan aka samo bindigogi biyar kirar AK-47, da bindigogi masu sarrafa kansu guda uku, da makamin harbo jiragen sama guda daya, da wata bindigar mai sarrafa kanta samfurin PKT, sannan aka lalata mota daya.