✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke hukunci kan karar da aka shigar da Shekarau ta cin kudin yakin neman zabe

Hukumar EFCC ba ta gabatar da kwararan hujjoji ba kan zargin da ta ke yi wa Shekarau.

A ranar Talata wata Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Kano, ta wanke tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau, daga zargin yin sama da fadi da kudin yakin neman zaben jam’iyyar PDP da suka tasarma Naira miliyan 950.

Tun a shekarar 2018 ne Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta shigar da karar Shekarau bisa zargin karkatar da kudaden da aka raba a gidansa yayin da ya ke Ministan Ilimi kuma jagoran PDP a jihar a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.

EFCC ta yi zargin cewa, Shekarau ya karbi Naira miliyan 25 a matsayin kason da ya samu yayin da aka raba kudin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jajibirin babban zaben kasa na 2015 wanda tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya nemi tazarce.

Da take yanke hukunci a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, Mai Shari’a Amina Wambai, ta riki cewa Hukumar EFCC ba ta gabatar da kwararan hujjoji ba kan zargin da ta ke yi wa Shekarau yayin zaman wata babbar kotu da aka gudanar a ranar 27 ga watan Satumban 2019 wanda Mai Shari’a Lewis Allagoa ya jagoranta.

Mai Shari’a Wambai ta ce Hukumar EFCC tun a wancan lokaci ta gaza gabatar da dalilai da ke nuna alakar Shekarau da kudaden da ake zargin ya yi ruf da ciki a kansu.

Haka kuma Kotun ta ce Hukumar EFCC ta gaza gabatar da hujjar da ke nuna cewa Shekarau ya taka rawa wajen raba kudaden a gidansa, inda ta jaddada cewa babbar Kotun da aka yi kararsa a gabanta ta nuna cewa kudin da aka karbo daga hannun tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison Maduekwe ya saba wa doka.

Lauyan Shekarau, Barista Abdul Adamu ya ce hukuncin da babbar kotun ta yanke ya wanke Tsohuwar Ministar daga duk wani zargi da tuhume-tuhume.

Shekarau wanda shi ne wakilin shiyyar Kano ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, EFCC ta yi zargin cewa laifin da ya aikata ya saba wa sashe na 16 da 18 cikin dokokin kudi na Najeriya.