✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa dan dambe hukuncin rataya a Adamawa

Kotu ta yanke wa dan damben gargajiyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe matarsa da tabarya

Wata babbar kotun Jihar Adamawa ta yanke wani dan damben gargajiya hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe matarsa a hanyar buga mata tabarya a kai.

An yanke wa fitaccen dan damben gargajiyar mai suna Thank-You Grim, daga kauyen Silli a Karamar Hukumar Guyuk, hukuncin ne bayan an gurfanar da shi bisa zargin aikata kisa.

Da yake yanke hukunci a ranar Talat, Babban Alkalin Jihar Adamawa, Mai Shari’a Nathan Musa ya ce kotu ta gamsu cewa Thank-You Grim ne ya kashe matarsa don haka ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai gabatar da kara, Salihu Muhammad, ya shaida wa kotun cewa dan damben ya kashe matar tasa ce ta hanyar kayar da ita sannan ya dauko tabarya ya buga mata a kai, ta ce ga garinku nan a ranar 24 ga watan Maris, 2018.

Aminiya ta samu bayanai cewa tun a 2018 ne ma’auratan suka daina zama tare saboda rashin daidaito a tsakaninsu.

Daga baya matar ta nemi mijin ya ba ta takardar saki, ta yi wani aure bayan ta sami wani manemi, wanda hakan ya fusata Grim.

Maimakon ya ba ta takardar saki sai ya nemi ta zo da kanta ta karba a gidansa, inda bayan ta je ya roke ta ta dawo su ci gaba da zama, amma ta ce allambaran.

Ana cikin haka ne rikici ya kaure a tsakaninsu har ya buga mata tabarya a kai ta rasu.

Lauyan mai kara, Salihu Muhammad, ya yaba da hukuncin a matsayin adalci.

A nasa bangaren, lauyan wanda ake kara, F.A. Ogbe, ya ce hukuncin ya yi daidai.