An yanke wa jarumar Kannywood hukuncin komawa Islamiyya | Aminiya

An yanke wa jarumar Kannywood hukuncin komawa Islamiyya

Sadiya Haruna
Sadiya Haruna
    Abubakar Muhammad Usman da Lubabatu I. Garba, Kano

Wata Kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta yanke wa wata jarumar fina-finai ta Kannywood hukuncin komawa makarantar Islamiyya.

An gurfanar da matashiyar mai suna Sadiya Hruna ne a gaban kotun, wadda ke zamanta a Sharada, bisa tuhumar amfani da kafafen sada zumunta da YouTube wajen yada hotuna da bidiyon batsa.

Wacce ake tuhumar ta amsa laifin da aka tuhume ta da aikatawa, wanda ya ci karo da sashe na 355 na kundin dokar Penal Code ta 2000.

Ranar Juma’a ne dai Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cafke jarumar, wacce ta yi shuhura a dandalin sada zumunta.

Hisbah ta ce ta cafke matashiyar ne saboda yada hotunan batsa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ali Jibril Danzaki, ya yanke mata hukuncin shiga makarantar Islamiyya ta Darul Hadith da ke Tudun Yola, a Kano na tsawon watanni shida a matsayin hukuncin laifin da ta aikata.

Kazalika, ya ce hukumar Hisbah da shugaban makarantar za su sanya ido kan halartar Islamiyyar.