An yanke wa malami hukuncin daurin rai-da-rai saboda yi wa ‘yar shekara 14 ciki | Aminiya

An yanke wa malami hukuncin daurin rai-da-rai saboda yi wa ‘yar shekara 14 ciki

Gwamnan Legas, Sanwo-Olu
Gwamnan Legas, Sanwo-Olu
    Bashir Isah

Wata kotu a Ikeja, Jihar Legas, ta yi wa wani malami daurin rai-da-rai bayan ta kama shi da lafin fyade da kuma banka wa wata ’yar shekara 14 ciki.

Mai gabatar da kara ya shaida wa kotun ceaw Joseph Ibanga, ya aikata laifin ne tsakanin watan Janairu da Maris na 2019.

A lokacin da take yanke hukunci, Mai Shari’a Abiola Soladoye ta ce, masu tuhuma sun gabatar wa kotun hujjojin da suka tabbatar da Joseph Ibanga ya aikata laifin fyade.

Soladoye ta ce: “Wadda aka yi wa fyaden karamar yarinya ce wadda ba ta san ciwon kanta ba.

“Hujjar da aka gabatar wa kotu ta nuna wanda ake kara ya sadu da yarinyar a inda take da zama tare da innarta, wanda hakan ya sa ta samu juna-biyu.

“Sannan rahoton asibiti ya gaskata abin da ya faru, sannan akwai hujja a gaban kotu da ta tabbatar da mai kare kansa ya aikata laifin.

“Yarinyar ta nuna mai kare kansa malaminta ne a gida, shi ne kuma ya yi ta lalata da ita da karfin tsiya.”

Mai Shari’ar ta ci gaba da cewa, “Mai kare kansa mugun mutum ne kuma mai rashin godiya. Ya ci zarafin yarinyar tare da karantar da ita shirme; ya haifar wa aikin karantarwa kallon banza, kuma hukuncin da aka yanke mishi zai zame mishi darasi.

“Don haka, kotu ta sami mai kare kansa da aikata laifin da ake tuhumar sa da aikatawa duba da hujjar da aka gabatar a kansa, sannan an yanke masa hukunciun daurin rai-da-rai.”

Haka nan, Mai Shari’ar ta ba da umarnin a saka sunansa a cikin kundin laifuka masu alaka da fyade na Jihar Legas.

Bayanai sun nuna an dauki Joseph Ibanga don ya rika karantar da yarinyar a gida ne sakamakon ta yi fashin makaranta na tsawon lokaci saboda lalurar rashin saurin kama karatu.

Masu tuhumar sun ce laifin da ya aikata ya saba wa Sashe na 137 Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015, wanda hukuncin hakan shi ne daurin rai-da-rai a kurkuku.