✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

Dalilai na shari’a sun tabbatar hukuncin kisa ta hanyar rataya ya wajaba a kan matashin.

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 35 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da aikata laifin kisan gilla.

A ranar Alhamis ce Kotun ta yanke wa Nura Gwanda hukuncin saboda laifin da aka same shi da shi na daba wa wani dan shekara 27 mai suna Mudan Ibrahim wuka, wanda a dalilin haka ajali ya yi kiransa.

Mai Shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud da ta yanke hukuncin, ta ce hujjoji da aka gabatar na tuhumar matashin babu shakku a kansu.

A cewarta, dalilai na shari’a sun tabbatar cewa hukuncin kisa ta hanyar rataya ya wajaba a kan matashin.

Tun da farko jami’in da ya gabatar da kara a gaban kotu, Lamido Sorondinki ya ce, wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Afrilun 2018 a Unguwar Fagge da ke birnin Dabo.

Sorondinki ya ce da misalin karfe 6.00 na yammacin wannan rana ce Nura ya ziyarci gidansu Mudan domin karbo bashin Naira dubu uku da wani dan uwansa ya bayar rance ga mamacin da ya yi alkawarin zai biya.

Ya ce, yayin neman biyan bashin ne sa’insa ta kaure tsakaninsu, inda Nura ya hau dokin zuciya kuma ya daba wa Mudan wuka a ciki da kuma bayansa.

“An yi gaggawar garzaya wa da Mudan zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda a nan Likitoci suka tabbatar da ya cika,” a cewar Sorondinki.

Sorondinki wanda ya gabatar da shaidu uku a gaban kotun, ya ce laifin da Nura ya aikata ya ci karo da sashe na 221 da ke kundin dokar kasa.

Sai dai Nura ya musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda lauyansa Najib Hamisu ya gabatar da shaida guda daya yayin zaman kotun.