✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa matashin da ya kashe kishiyar mahaifiyarsa hukuncin rataya

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa.

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa.

A zaman kotun na ranar Laraba, Mai Shari’a Shari’a Aisha Mahmud, yi karatun baya, inda ta samu matashin da laifin daddatsa kishiyar mahaifiyarsa da adda, sannan ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun da ke zaman ta a Sakatariyar Audu Bako ta ce ta gamsu da tuhumar da ake masa bayan samun cikakkun shaidu, ta kuma yanke masa hukuncin rataya karkashin sashi na 221 na kundin dokar laifuka na Jihar Kano.

Tun da fari, an gurfanar da Sagiru Wada ne bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa, Zainab Dan-Azumi, da wata adda shekaru takwas da suka gabata.

Lauyan wanda ake kara, Barista Rabi’u Abubakar, ya shaida wa kotun cewa matashin na da tabin kwakwalwa, amma ta yi watsi da hujjar bisa shaidun da ta yi amfani da su.

Lauyan gwamnati, Barista Tijjani Ibrahim, ya ce kotu ta yi nazari ta ga babu wani dalili da za a ce yana da motsi a kwakwalwarsa kuma hakan bai gamsar da ita ba, shi ya sa ta yi watsi da rokon.

A nasa bangaren, lauyan wanda ake kara ya ce za su zauna su yi nazari kuma su ga mataki na gaba da za su dauka.

Ali Mandawari, dan uwan marigayiyar ne, ya ce sun yi farin ciki da hukuncin kuma gaskiya ta yi halinta.