✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa mutum 2 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Ekiti

A ranar Talata wata Babbar Kotu mai zamanta a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ta yanke wa wasu mutum biyu, Makinde Kola da Haruna Bika…

A ranar Talata wata Babbar Kotu mai zamanta a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ta yanke wa wasu mutum biyu, Makinde Kola da Haruna Bika hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Tun ranar 28 ga Fabarairun da ya gabata aka gurfanar da wadanda lamarin ya shafa da ake tuhuma da aikata laifuka shida.

Kotun karkashin jagorancin Alkali Olalekan Olatawura, ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta sami mutum biyun da aikata laifukan da suka hada da hadin baki da fashi da makami da fyade da kuma garkuwa da mutane.

Lauyar mai tuhuma, Misis Olasanmi Oluwaseun, ta fada wa kotun wadanda ke kare kansu sun yi wa Taiwo Oni da Mohammed Ayomide fashi a ranar 6 ga Oktoban 2021, a sansanin Idi Mango da ke Ilasa-Ekiti, inda suka kwace musu wayoyi.

Kazalika, ta ce sun kuma yin fashi inda suka raba wani mai suna Mista Adejuwon Gbenga da kudinsa har  Naira 31,000.

Ta kara da cewa duka a cikin rana daya, sun yi wa wata mata mai danyen goyo fyade. Kuma sun aikata hakan ne dauke da adda da bindiga.

Lauyar ta ce duka laifukan da suka aikata sun saba wa Sassa na 516 da 401 (2) na Kudin Dokokin Laifuka Cap. C16, na Dokokin Jihar Ekiti na 2012.

Kazalika, ta ce laifukan sun saba wa Sashe na 2 (2) na Dokokin Cin Zarafin Mata na Jihar Ekiti na 2019 da kuma Sashe na 3 (a) na Haramcin Garkuwa da Ta’addanci na Dokokin Jihar Ekiti na 2015.

Oluwaseun ta gabatar wa kotun da gamsassun shaidu da hujjoji wanda hakan ya sanya kotun yanke wa masu laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.

(NAN)