✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa sojan Siriya hukuncin daurin rai-da-rai a Jamus

An samu Raslan da laifin kisan gilla da azabtar da mutane ba bisa ka'ida ba.

Wata kotu a kasar Jamus ta yanke wa wani tsohon sojan Siriya hukuncin daurin rai-da-rai, sakamakon kama shi da laifin kisan gilla da azabtar da mutane, a wata shari’a mai tarihi a kasar.

Kotun dai ta yanke wa Kanar Anwar Raslan mai shekara 58 hukuncin daurin rai-da-rai ne, bayan ta kama shi da laifin yi azabtarwa da kuma hallaka mutum 27 ba bisa ka’ida ba a Gidan Yarin Al-Khatib da ke birnin Damascus daga shekarar 2011 zuwa 2012.

Masu shigar da karar sun kuma tuhumi Raslan da kin tsawatarwa yayin da aka yi wa wasu mutum 58 kisan gilla tare da azabtar da sama da 4,000 duk a gidan yarin na Al-Khatib.

An dai gabatar da shaidu sama da 80, cikinsu har da guda 12 da aka fara zargin su tare da cin amanar kasar da kuma ’yan kasar ta Siriya da ke zama a kasashen Turai da dama, don bayar da shaida a kansa.

Tuni dai Shugaban Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta ‘Human Rights Watch’, Kenneth Roth, ya yi maraba da hukuncin, inda ya ce wadanda suka rasa rayukansu a karkashin ikonsa, ba tare da hakkinsu ba sun samu adalci.

A shekarar 2012 ne Raslan ya nemi mafakar siyasa a Jamus bayan da aka fara za rgin shi da yunkurin cin amanar kasarsa.