✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa ’yan sanda 2 da wasu mutum 3 hukuncin kisa a Akwa Ibom

Kotun ta yanke musu hukuncin ne bisa yin garkuwa da wani dillalin shanu.

Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom da ke zamanta  Karamar Hukumar Ikot Ekpene, ta yanke wa wasu jami’an ’yan sanda biyu da karin wasu mutum uku hukuncin kisa.

Kotun dai ta yanke musu hukuncin ne a ranar Juma’a bisa aikata laifin garkuwa da wani dillalin shanu na birnin Uyo, Alhaji Muhammad Barkindo.

Da take yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a Eno Isangedighi, ta ce kotun ta same su da aikata laifin da ake zarginsu da shi.

“Masu shigar da kara sun gamsar da kotu cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin sace mutumin ranar 25 ga watan Nuwamban 2011, laifin da hukuncinsa kisa ne, kamar yadda Dokar Tsaro ta Jihar Akwa Ibom ta 2009 ta tanada,” inji Mai Shari’ar.

’Yan sandan dai, Kofur Friday Udo da Kofur Saturday Okorie, ’yan asalin Kananan Hukumomin Ikot Inyang da Ikot Etenge ne dake Jihar, kuma tuni aka sallame su daga aiki.

Sauran wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Walter Jack Udo da Udo Okon Etim da kuma Udo Moses, dukkansu ’yan asalin Jihar ta Akwa Ibom.

An dai yi amfani da gidan Udo Okon wajen ajiye wanda aka sace din sannan aka bukaci Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansarsa.

Hukuncin dai ya kawo karshen shekara 10 ana tafka shari’a a kan lamarin.