✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yaye mutum 4,360 da suka ci gajiyar N-Power a Kano

An yi bikin yaye wanda suka ci gajiyar shirin a Jami'ar KUST da ke Kano.

Akalla mutum 4,360 wadanda suka ci gajiyar shirin N-Power daga shiyyar Arewa Maso Yamma, aka yaye a Jihar Kano.

Bikin yaye wanda suka ci gajiyar ya gudana ne a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil a Kano.

Da take yin jawabi ga wadanda suka ci gajiyar, Ministar Agaji da Jin Kai, Sadiya Umar Farouq, ta ce shirin wani yunkuri ne na cire miliyoyin ’yan Najeriya daga cikin kangin talauci tare da samar musu da abin yi.

“Na yi farin cikin yin bankwana da daliban N-Knowledge daga yankuna shida na Arewacin kasar nan. Zan fara da taya wanda suka samu damar shiga sabon tsarin na N-Power,” Abubakar Hashim, hadimi na musamman da ta wakilci ministar a wajen bikin yaye wanda suka ci gajiyar shirin.

Kazalika, a cewarsa akwai ragin mutum 7,000 da ake son kara ba wa dama musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar domin cike gurbin mutum 20,000 a kashin farko na shirin.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin, Abubakar Musa daga Jihar Kaduna, ya gode wa Gwamnatin Tarayya da kuma Ministar kan irin yadda aka tallafi rayuwarsu.