✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi bikin cika shekaru 40 da fara yaye daliban aikin Jarida a Jami’ar Bayero

Duk wani jijjige a harkar sadarwa a Najeriya to daga wannan Jami’a ya fito.

An gudanar da bukukuwan cika shekaru 40 da fara yaye dalibai a sashen koyon aikin Jarida na Jami’ar Bayero, Kano.

Taron wanda aka kammala a ranar Litinin, tsaffin daliban sashen irin su Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da tsohon Kakakin rundunar kasa da sojojin Najeriya Sani Usman Kukasheka sun halarta.

A shekarar 1978 ne aka bude sashin horas da dalibai a kan aikin Jarida da yada labarai na Jami’ar ta Bayero Kano, kuma an yaye rukunin farko na daliban a shekarar 1981.

Wadanda aka yaye a bara, wato shekara ta 2021 sune rukunin dalibai na 40 da sashen ya yaye bayan kafa shi.

Ko da yake, kasa da shekaru 10 da suka shude, sashen ya rikide zuwa tsangaya kuma gabanin haka ya yaye dalibai masu digiribiyu zuwa sama.

Muryar Amurka ta ruwaito Dokta Abubakar Shehu Minjibir da ke zaman shugaban kwamitin tsare-tsaren bukukuwan yana karin haske dangane da sauye-sauyen da sashen ya samu.

“An samu sauye-sauye da damar gaske misali kamar bangaren malamai yawan su da ingancin su, kayan aiki da kuma yawan daliban da ake horaswa a kuma yaye a wannan sashe, sannan daliban da aka yaye gudumuwar da suke bayar wa wajen yada labarai.”

Farfesa Abdallah Uba Adamu, guda ne cikin shehunnan Malaman da ke koyarwa a wannan fanni ya yi tsokaci a kan tasirin da sashen ya yi a cikin shekaru 40.

“Wato wannan sashe ya yi tasiri sosai, saboda duk wani jijjige a harkar sadarwa a Najeriya to daga wannan Jami’a ya fito, saboda haka muna alfahari da wannan wuri da kuma irin gudumuwar da ya bayar na fitar da mutane zakakurai wadanda suke aiki sosai.”

Masu tsara taron dai, sun yi amfani da wannan dama wajen kaddamar da kungiyar tsaffin daliban da wannan sashen na koyon aikin jarida na Jami’ar Bayero Kano ya yaye.

A jawabinsa, Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ke cikin rukunin daliban da suka kammala karatu a sashen shekaru 38 da suka gabata, ya albarkaci taron.

“Mun yi farin ciki da saduwa da dukkan tsoffafin dalibai da na gaba damu da wanda muke sawu daya, da wandanda muka zarta.

“Allah ya maimaita mana irin wannan taro. Malamanmu, iyayenmu da shuwaganninmu da ku ka dage wajen ilmantar damu da tarbiyantar da mu, Allah Ya fi mu yabawa.”

Sashin Hausa na Muryar Amurka wadda na cikin kafofin labaru da aka karrama da lambar yabo a yayin jerin bukukuwan da aka yi domin murnar wadannan shekaru 40.