✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da basarake a Kwara

An sace basaraken akan hanyarsa ta zuwa gona.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Mogaji Eburu, Dokta Zubair Folorunsho Erubu a Jihar Kwara.

Sai dai ’yan sanda sun ce ba a samu masaniyar inda ’yan bindigar suka boye shi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da shi ne a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gona a tsakanin Ilorin da Afon a ranar Alhamis.

Erubu tsohon ma’aikacin lafiya ne da ya yi aiki a gidan gwamnatin jihar.

Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar Okasanmi Ajayi, ya fitar ta ce Kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.