✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Dagaci a Katsina

An sace shi ne bayan ya sayar da amfanin gonarsa a kasuwa.

Wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da Dagacin garin Dutsin Safe da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina, jim kadan da sayar da amfanin gonarsa a kasuwa.

Anyi garkuwa da Alhaji Jabiru Magajin garin Dutsin safe ne bayan ya sayar da kayan amfanin gonar tasa a kasuwa, kamar yaddawata majiya daga yankin ta tabbatar wa Aminiya.

Majiyar, wacce ke da kusanci da basaraken ta ce ’yan bindigar da suka kai samamen, sun tunkari gidan Dagacin ne kai tsaye inda kuma suka bukaci da ya basu kudin da ya sayar da amfanin gonar, wadanda suka haura miliyan daya, sannan suka tisa keyarsa zuwa daji.

A cewar majiyar, babu wanda suka harba ko suka tafi da shi a garin in ban da Dagacin, wanda wasu ke zargin akwai sa hannun wasu makusantansa a lamarin.

’Yan bindigar dai, wadanda da aka ce yawan su ya kai bakwai, biyar daga cikin su na dauke da bindigogi.

Gari na Dutsin Safe dai bai wuce nisan kilomita biyar ba tsakaninsa da birnin Katsina.

“Rabon da a kawo mana irin wannan hari a yankin baki kusan shekara uku zuwa hudu ke nan, tun lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari a garin, inda babu wanda ya tsira daga cikinsu,”, inji wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunanshi.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne ’yan bindigar suke je garin Daddara Alhaji, inda suka kashe Magajin Garin ’Yangayya, Alhaji Jafaru tare da hadiminsa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba mu samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambi Isa, ba saboda matsalar hanyar sadarwa.