✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da DPO a Filato

’Yan bindiga sun yi garkuwa daBabban DPO na ’yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Pankshin ta Jihar Filato. 

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Babban DPO na ’yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Pankshin ta Jihar Filato. 

Aminiya ta samu rahoto cewa washegarin da SP Lareee ya fara aiki a matsayin DPO ne ’yan bindigar suka yi awon gaba shi a otel din WOKTORI da ke garin Pankshin a ranar Alhamis.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, amma jami’in ya ce masa “ba zan iya magana a kan batun ba, yanzu haka ina halartar wani taro ne.”

Kawo yanzu dai babu bayani game da inda maharan suka tafi da jami’in.