✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da hakimi da mutum biyu a Plateau

Wasu ’yan bindiga  sun yi garkuwa da Alhaji Shehu Sulaiman, Basaraken Bogghon kuma Hakimin Kanam a jihar Fitato. Majiyarmu ta samu rahoton cewa, ’yan bindigar…

Wasu ’yan bindiga  sun yi garkuwa da Alhaji Shehu Sulaiman, Basaraken Bogghon kuma Hakimin Kanam a jihar Fitato.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun fara yin garkuwa da maidakin Hakimin Bashar da direbansa tun a ranar Alhamis.

Hakimin Bashar, Ali Adamu Idris ne ya tabbatarwa  da wakilinmu hakan ranar Litinin, inda ya ce masu garkuwan sun kai harin ne a tsakar daren ranar Alhamis.

Hakimin Bashar, ya bayyana sunan maidakin nasa wanda aka sace mai suna Asma’u Usman da direbansa mai suna Auwalu Kakirani.

Hakimin Bashar ya kara da cewa, bayan yin garkuwan da mutum biyun ’yan bindigar sun yi ta harbi a yankin da suka shiga don razana jama’a.

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Filato ta Tsakiya Hezekiah Dimka ya fitar da jawabin takaicinsa ta hannun maitaimaka masa na musamman Shehu Kanam, inda ya yi Allah wadai da sace Basarake Pankwal Bogghom a gundumar Kanam tare da iyalan Hakimin Bashar biyu da aka yi garkuwa da su.