✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi garkuwa da jagoran PDP a Kaduna

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Jam'iyyar PDP na Gundumar Dan Mahawayi da wani mutum daya ana gab da zabe.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Jam’iyyar PDP na Gundumar Dan Mahawayi da wani mutum daya ana gab da zabe.

Harin da aka kai da misalin karfe 11 na dare ranar Lahadi shi ne karon farko ke nan da aka sace muane a gundumar Dan mahawayi da mutum daya ana gab da zabe.

Wani shugaban ’yan banga a yakin ya shaida wa wakilinmu cewa bayan kammala zagayen kamfen na dan takarar Majalisan Tarayya mai wakiltar Giwa da Birrinin Gwari, ne al’amarin ya faru.

Ya ce maharan da ake kyautata zanton suna cikin ayarin kamfe din ne sun kutsa kauyen ne da dare suka dauke Alhaji Bala Alhassan Marafa, shugaban jam’iyyar PDP na gundumar, da Alhaji Sulaiman Isyaku Mai Suga, wadanda su biyun shuwagabanni ne a yankin.

Al’ummar garin Dan Mahawayi sun ce wannan shi ne karon farko da ’yan bindigar suka yi garkuwa da wani mutumin garin.

Sun ce a bayan ’yan bindigar sukan shiga garin domin neman abin biyan bukatu, ko shan shayi da burodi, kuma a wani lokacima ba a karban kudinsu saboda gudun haka, amma sai gashi a sun fara dauke mutane a garin.

Dan sintirin wanda ya roki a boye sunansa ya kara da cewa har yanzu wasu yankunan Karamar Hukumar Giwa na fama da matsalar tsaro inda kusan kullum sai an sami labarin an sace wani mutum ko mutane.

Mun nemi jin ta bakin kakakin ’yan sandar Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, amma ya ce wakilinmu ya ajira shi zai kira, amma har lokacin hada wannan rahoton ba mu ji daga gare shi ba.