✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da limamin coci a Mali

An dora zargi kan kungiyar IS mai tarihin garkuwa da ’yan kasashen waje don samun kudin fansa.

Wasu da ake zargin masu zafin kishin addini sun yi garkuwa da wani limamin coci dan kasar Jamus a Bamako, babban birnin kasar Mali.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10 da aka sace wani dan kasar yammacin duniya a Mali.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin yin garkuwa da limamin cocin, wanda ya shafe fiye da shekaru 30 a Mali.

Sai dai Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa tuni aka dora zargi kan kungiyar IS mai tarihin garkuwa da ’yan kasashen waje don neman kudin fansa.

Rahotanni sun ce an gano motar Hans-Joachim Lohre a Bamako, babban birnin kasar Mali kusa da makarantar da yake koyarwa.